Dan Gidan Salihu Sagir Takai Ya RasuAllah Ya yi wa Ibrahim Salihu Sagir Takai rasuwa,  yau Lahadi bayan gajeriyar jinya sakamakon hadari da ya samu akan hanyar dawowar sa daga sansanin masu bautar kasa na jihar Zamfara. 

Za a yi jana’izar sa gobe 21/8/2017 a gidan mahaifinsa Malam Salihu Sagir Takai dake ‘Yankaba da Misalin karfe 8:00 na Safe.

You may also like