Dan gidan Tinubu ya mutu a wani yanayi mai sarkakiya


Bola Ahmad Tinubu, jagoran jam’iyar APC na kasa ya rasa dansa na farko.

Wata majiya ta shaidawa jaridar the Cable cewa,Jide Tinubu, marigayin yana cikin koshin lafiya amma ya mutu ranar Laraba babu zato babu tsammani.

“Lafiyarsa kalau ya zuwa daren jiya amma mumbar komai a hannun Allah,” majiyar ta ce.

Henry Ajomale, shugaban jam’iyyar APC na jihar Lagos ya tabbatar da faruwar lamarin inda yayi kira ga ya’yan jam’iyyar da su mika ta’aziyarsu ga jagoran jam’iyar.

Har yanzu dai babu cikakken bayani akan mutuwar tasa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like