Dan kaso ya bindiga jami’an kotu a Amirka


Wani fursuna mai suna Micah Johnson bakar fata kana tsohon soji ya bindige wasu jami’an kotu biyu tare da jikkata dan sanda daya a kotun birnin Michigan

 

A Amirka wani dan kaso ya bindige har lahira wasu jami’an kotu biyu tare da jikkata wani dan sanda daya a cikin wata kotun birnin Michigan a daran jiya Litanin, bayan da ya yi nasarar kwace bindigar wani jami’i a daidai lokacin da ake shirin mayar da shi daga kotun zuwa gidan kaso.

Hukumomin ‘yan sanda na birnin sun sanar da bindige mutuman dan shekaru 25 mai suna Micah Johnson bakar fata kana tsohon soji bayan da ya yi yinkurin tserewa daga hannun jami’an ‘yan sandar da ke kula da shi.

Wannan lamari ya zo ne kwanaki hudu bayan kisan gillar da wani dan bindiga ya yi wa wasu jami’an ‘yan sandar kasar ta Amirka guda biyar a birnin Dallas na Kudancin kasar lokacin wata zanga-zangar nuna adawa da amfani da karfin da ya wuce kima da ‘yan sanda ke yi kan bakar fata a kasar ta Amirka.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like