A kalla mambobin Civilian JTF uku aka kashe wasu 17 kuma suka jikkata a wani harin kunar bakin wake da aka kai ranar daren litinin a Maiduguri babban birnin jihar.
Joseph Kwaji, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na dare a yankin Muna Delti dake wajen birnin Maiduguri.
Kwaji ya bayyana cewa dan kunar bakin waken da ke kan keke ya tayar da bom din dake jikinsa inda ya kashe kansa tare da mambobin Civilian JTF uku.
Ya ce wasu mutane 17 kuma sun samu raunuka a fashewar bom din, ya kara da cewa wadanda suka jikkata an dauke su ya zuwa Asibitin Koyarwa Na Jami’ar Maiduguri domin samun kulawa.
A cewarsa tawagar jami’an yan sanda dake kula da abubuwa masu fashewa sun gudanar da bincike a yankin kuma tuni al’amura suka cigaba da gudana kamar yadda aka saba.