Dan kunar Bakin wake ya kashe mahaifinsa a hari kan masallaci a Borno


Wani matashi dan kunar baƙin wake ya kashe mutane 11 ciki har da mahaifinsa a wani masallaci dake Gamboru, jihar Borno.

Jaridar The Cable ta gano cewa lamarin yafaru ne da asubahin ranar Laraba.
Lawan Abba wani mazaunin Gamboru ya fadawa kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa mutane 10 aka kashe wasu shida kuma suka jikkata a harin.
Abba ya bayyana cewa dan kunar baƙin waken ya shiga cikin taron jama’ar dake masallacin yayin da mutane suka taru za su gabatar da sallar asuba inda ya tayar da bom din.

“Dan kunar bakin waken yafito ne daga garin Gamboru. Ya bar iyayensa inda yabi yan ta’addar dake cikin daji,”Abba yace.

” Ya shiga cikin masallacin ya tarwatsa kansa filla-filla, da kuma mutane 10 ciki har da mahaifinsa.”

Harin kunar baƙin wake a bune da yadade yana ciwa jami’an tsaro tuwo a kwarya duk da ikirarin bada suke na samun nasara kan ya’yan kungiyar ta Boko Haram.

You may also like