Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane A Wani Masallaci A Maiduguri Wani ɗan kunar bakin wake da ake kokarin hana shi shiga masallaci ya rungumi wani mutum inda suka mutu tare a garin Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Wani ganau ya shaidawa majiyarmu cewa dan kunar bakin waken ya so ya shiga masallaci amma wani mai binciken mutane kafin ya shiga ya haska shi da tocila, ganin haka ne yasa dan kunar bakin waken ya tunkare shi ya rungume shi suka mutu tare.
Ganau din ya kara da cewa sun ji karar wani abu suka garzaya wajen suka ga gawarwaki sun yi kaca-kaca.
Wannan dai shine karo na uku da ‘yan kunar bakin wake suka tashi bam a birnin Maiduguri. A kwanakin baya wata ‘yar kunar bakin wake ta tashi bam inda mutum hudu suka mutu ciƙi har da Farfesa.

You may also like