Dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna ya sauya sheka daga jam’iyar APC ya zuwa PDP


Adams Jagaba, wakili a majalisar wakilai daga jihar Kaduna ya sauya sheka daga jam’iyar APC ya zuwa PDP.

Jagaba, wanda ke wakiltar mazabar Kachiya/Kagarko ya bayyana sauya shekar tasa ya yin zaman majalisar na yau Laraba.

A wata wasikar sauya shekar tasa da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara ya karanta, dan majalisar ya bada hujjar rikicin shugabanci a jam’iyar a matsayin dalilinsa na sauya shekar.

Jagaba shine shugaban kwamitin majalisar kan harkokin cikin gida.

Tun a cikin watan Janairu be dan majalisar ya nuna alamun zai fice daga jam’iyar baya da jam’iyar APC reshen jihar Kaduna ta dakatar da shi.

A wancan lokacin Jagaba ya bayyana APC a matsayin wani jirgin ruwa dake nutsewa inda ya ce ba zai yadda ya halaka a ciki ba.

You may also like