Dan Sanda Ya Bindige Wani Har Lahira akan Naira 50.


Wani jami’in dan sanda a jihar Binuwai ya bindige wani dan achaba har lahira akan rigimar naira 50.
Majiyarmu ta ba mu labarin cewa wannan al’amari ya faru akan hanyar Aliade zuwa Awajir a lokacin da marigayin mai suna Friday ya sa baki akan rigimar bayar da naira hamsin a matsayin na goro da jami’in Dan sandan ya bukaci wani abokin sana’arsa ya ba shi.
Majiyar ta mu ta kara da cewa shiga tsakani da Friday ya yi bai yi wa Dan sandan dadi ba, kuma wata-wata ya dirka masa albarusai a goshi inda ya fadi nan take ya mutu.
Mutuwar Friday ta sanya matasan yakin gudunar da zanga zanga aanda har ya kai ga yunkurin bankawa tashar ‘yan sandan da jami’in dan sandwn yake aiki wuta.
Da yake magana dangane da wannan al’amari mai magana da yawun ‘yan sanda jihar ta Binuwai, Mista Moses Yamu, ya ce ba su sami wannan labarin ba tukuna amma ya ce za su gudanar da bincike.

You may also like