Dan Sanda Ya Harbe Soja A Jihar Delta


Wani dan sanda da ba san ko waye ba a Najeriya da ke aikin gadin wani wurin hakar man fetur din kamfanin Shell an ruwaito cewa ya harbe wani soja har lahira a kauyen Odimodi dake a karamar hukumar Burutu ta jihar Delta dake a kudu maso kudancin kasar nan.

Majiyar mu dai ta ruwaito mana cewa lamarin ya faru ne a a ranar Asabar din da ta gabata biyo bayan wata ‘yar gardama da ta rikide ta zama husuma a tsakanin su.

Sai dai kawo yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabin rigimar ta su ba amma dai an hango su suna ta fada da cacar baki kafin daga bisani dan sandan ya narka masa harsashe wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sa.

You may also like