“Dan shekara 35 ya yi wa yarinya mai shekaru 11 fyade gami da yi mata ciki a jihar Kano. Likitoci sun tabbatar da yarinya ba za ta iya haihuwa ba sai dai a yi mata tiyata. Wannan labarin mai sosa zuciya an yada shi ne a shirin Inda Ranka.. na gidan rediyo Freedom. A cewar jagoran shirin Nasiru Salisu Zango ya bayyana wannan labarin ne domin neman daukin Hukumar kare hakkin bil Adama. Idan kuma akwai wanda zai iya taimakawa zai iya tuntubar gidan rediyon ko jagoran shirin.