DAN SIYASA NA GARI SHINE WANDA YA RIKE JAMA’ARSA TARE DA TAIMAKON SU TA KOWANNE HALI – DAKTA AHMAD GUMI



An bayyana Siyasa a matsayin hanya ce ta jagoranci da cigaban Al’umma, sabanin yadda wasu ke ganin Siyasa a matsayin wata hanya ta yaudara da satar kudin Gwamnati.

Mashahurin Malamin Addinin Musulunci nan mazaunin garin Kaduna Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi a yayin wani taro na yiwa jama’a masu fama da lalurorin rashin lafiya daban daban aikin tiyata kyauta, wanda tsohon Dan Majalisar wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa a Majalisar kasa Abuja Alhaji Shehu Usman ABG ya dauki nauyi, wanda ya gudana a Babban Asibitin garin Unguwar Shanu dake yankin karamar hukumar Kaduna ta Arewa. 

Dr Gumi ya yaba da kokari na tsohon Dan Majalisar duk da cewar ba ya kan kujera amma Jama’ar shi na zuciyar shi, har ya dauki nauyin wannan aikin lallai wannan abin a yaba ne, inda ya bayyana muhimmancin abinda ya kamata ‘yan siyasa suyi kenan taimakon Al’umma ba yawace yawace Kasashen waje ba, sannan ya bukaci iyaye su bar ‘ya’yan su musanman Mata su samu ilimi na kiwon lafiya, domin taimakon Mata Musulmi ta fuskar kula da lafiyar su idan sun halarci Asibiti.

A jawabin da ta gabatar Dr Aisha Mustafa daga Asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, tace cututtukan da suka addabar Mata a wannan lokaci sun hada da matsalar ciwon Daji na mahaifa da kuma kaikayin Farji, inda ta bukaci Mata da su rinka ziyarar Asibitoci domin a rinka bincike da duba lafiyar su, idan so samu ne duk bayan watannin Shidda, domin kamar yadda ta bayyana matsalolin sun fi addabar Mata a yankin Arewa idan aka kwatanta da kudancin Nijeriya, sannan ta kara godewa Honorabul Shehu ABG akan daukar gudanar da ayyukan tiyatar kyauta da ya yi. 

A jawabin shi Honorable Shehu ABG wanda shine mai bada shawara ga Shugaban Majalisar dokokin Tarayya Yakubu Dogara akan harkokin Majalisa, yace Babban dalilin da ya ja hankalin shi akan wannan aiki shine, lura da halin da jama’a su ke ciki na fama da talauci ga kuma rashin lafiya da ke addabar su, shi ya sanya ya dauki nauyin aiwatar da wannan aiki kyauta ga jama’a, kuma kamar yadda kowa ya sani zaman da yayi a Majalisa a shekarun baya ya aiwatar da wadannan ayyuka lokuta da dama, kuma zai cigaba da gudanar da wadannan ayyuka anan gaba.

Malam Nasiru Bagobiri da Malama Kulu Maijidda suna daga cikin dubban Mutanen da su ka ci gajiyar aikin tiyatar, a zantawar da akayi da su sun nuna godiyar su gami da jin dadin sune akan aikin tiyatar da akayi musu, inda suka roki sauran ‘Yan siyasa da yin koyi da Honorabul Shehu ABG na taimakon jama’a musanman marasa karfi.

You may also like