Mutumin da yayi sanadiyar rasa rayuka da akayi a birnin london bayan harin da yakai kusa da harabar majalisar birtaniya, dan asalin kasar ne, Firaminista Therasa May ta bayyana haka a yau alhamis.
Dan ta’addan yakai harin ne a kusa da majalisar kasar a jiya laraba inda ya kashe mutane 3, sannan ya jikkata wasu mutane da dama ciki har da jamian tsaro.