Dan Uwan, Nmandi Kanu, Jagoran Kungiyar IPOB Ya Nemi Sojojoi Su  Basu Gawarsa Idan Sun Kashe Shi 


Emmanuel, kani ga Nmandi Kanu, jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, ya nemi sojojoi da su fito da gawar Nmandi Kanu idan har sun kashe shi. 

Kanu da iyayensa ba a gansu ba a bainar jama’a tun bayan da sojoji suka mamaye gidansu a Afarakwu dake jihar Abia a ranar 14 ga watan Satumba. 

Da yake magana a madadin iyalin, a ranar Talata, Emmanuel yace yana da yakinin cewa dan uwansa yafada hannun sojojin. 

“Ko dai sojoji sun kama shi ko kuma sun kashe shi lokacin da suka kawo hari gidan mu. Idan sun kama shi to su damka shi hannun yan sanda idan kuma sun kashe shi to su fito da gawarsa saboda ganin karshe da akayi masa shine yan mintoci kadan kafin zuwan sojojin,”yace.

Amma kuma rundunar sojin ta musalta cewa tana tsare da Kanu.

Wani da ya dauki kiran da akayi zuwa daya daga cikin lambar wayar da sojojin da suke gudanar da atisayen ‘Operation Python Dance ‘suka bawa jama’a,  yayi watsi da tunanin da jama’a sukeyi cewa Kanu yana hannun rundunar. 

 “Kanu baya tsare a hannun mu,” ya fada cikin kakkausar murya. 

Dan uwan Kanu yace sun shafe makonni biyu kenan  suna neman jagoran kungiyar ta IPOB da mahaifinsa amma babu wani labari da suka samu.

Yayi kira ga shugabannin kasashen duniya kan su lallaba hukumomin Najeriya da su saki iyayensa da kuma shugaban na IPOB. 

Mahaifin Kanu shine basaraken gargajiya na Afarakwu.

A makon da ya gabata ne masu rike da sarautun gargajiya wadanda suka fito daga karamar hukumar Umuahia ta Arewa suka bukaci sanin inda mahaifin Kanu da maidakinsa suke. 

You may also like