Dan wasan ƙwallon ƙafar ƙungiyar Kano Pillars, Chinedu Udoji ya mutu a hatsarin mota


Mai tsaron baya na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Chinedu Udoji ya mutu.

Ɗan wasan ƙwallon ƙafar ya mutu a safiyar ranar Litinin sanadiyar haɗarin mota da ya rutsa da shi a cikin kwaryar birnin Kano.

Udoji na kan hanyarsa ta zuwa gidansa dake unguwar Badawa lokacin da hatsarin ya rutsa da shi akan titin Bompai dake cikin birnin na Kano bayan da ya kai wa ƴan tsohuwar ƙungiyarsa ta Enyimba FC ziyara.

Udoji ya dawo ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars shekaru biyu da suka wuce daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enyimba.

Marigayin kwararren mai tsaron baya ne kuma shine aka bawa lambar gwarzon ɗan wasa, a wasan mako na 9 a gasar cin  kofin ajin kwararru na ƙasa da ƙungiyar ta kara da Enyimba inda suka tashi kunnen doki 1:1.

You may also like