Dan Wasan Nijeriya, Onazi Ya Tallafawa ‘Yan Super Falcons Da Naira Miliyan 1


 

Dan wasan Super Eagles, Ogenyi Onazi ya mika agajin Naira miliyan guda ga ‘yan wasan Super Falcons da suka yi nasarar lashe kofin Afirka ajin mata makonnin da suka gabata kuma gwamnatin Nijeriya da hukumar kwallon kafa ta kasar suka kasa biyansu hakkokinsu wanda har hakan ya sanya ‘yan matan suka yi zanga-zanga zuwa fadar majalisar wakilan kasar

 

Wani makusacin Onazi ya bayyanawa wata kafar yada labarai ta Afirka cewa Onazi da ke taka leda a kasar Turkiyya ya bayyana takaicinsa ga halin rashin karramawa ga ‘yan wasan suka samu daga gwamnati da hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF

“Onazi mutumin kirki ne, bayan duba da ya yi da halin da ‘yan matan da suka wakilci Nijeriya a kwallon kafa a gasar cin kofin nahiyar Afirka na rashin kulawa da rashin biyansu hakkokinsu, Onazi ya mika tallafin Naira miliyan 1 ga ‘yan matan don su rage radadin halin da suka samu kansu a ciki” a cewar majiyar
onaziP.JPG

Onazi hr ila yau ya baiwa ‘yar wasa da ta samu rauni naira dubu 200

You may also like