
Dangin Indiyawan – da aka samu gawarwakinsu a wani kogi da ke kusa da kan iyakar Amurka da Canada a makon jiya – sun ce har yanzu suna cikin kaɗuwa, da jimami.
An gane huɗu daga cikin gawarwaki takwas da ‘yan sanda suka samu a kogin St Lawrence cikin makon da ya gabata.
Hukumomi sun ce gawarwakin da aka gano na wasu iyalai biyu ne daga ƙasashen Indiya da Romaniya, waɗanda aka yi amanna cewar suna ƙoƙarin tsallakawa zuwa Amurka.
An bayyana sunayen Indiyawan da Pravin Chaudhary mai shekara 50, da matarsa Diksha mai shekara 45, sai ‘ya’yansu biyu, Vidhi mai shekara 24 da ƙaninta Meet mai shekara 20.
Iyalan sun taso ne daga ƙauyen Manekpur Dabhala a gundumar Mehsana a jihar gujarat da ke yammacin Indiya.
BBC ta ziyarci ƙauyen wanda har yanzu ke cike da alhini da damuwa game da rasuwar iyalan.
Dan uwan Pravin Chaudhary mai suna Jasubhai Chaudhary ya ce tun a ƙarshen mako ya fara shiga damuwa, a lokacin da yake kallon labarai a talabijin, inda ya ga labarin gano gawarwakin wasu Indiyawa huɗu.
Ya ce, ”daman mun shiga fargaba da ruɗani sosai, kasancewar idan an kira wayoyinsu kiran ba ya shiga tun bayan tafiyarsu.”
Asalin hoton, Reuters
Fargabar iyalan ta tabbata bayan da ‘yan uwansu da ke zaune a Amurka suka samu sakon email daga ‘yan sandan Canada kan rasuwar ‘yan uwan nasu.
Yayin da Jasubhai Chaudhary ke wannan maganar, mutanen ƙauyen na ci gaba da tururuwa zuwa gidansa domin yi masa ta’aziyya.
Makwabcin iyalan Sanju Chaudhary , ya ce Pravin Chaudhary mutumin kirki ne, ”manomi ne da ke sana’ar sayar da madara a yankunan da ke kewayen ƙauyen,” in ji shi.
Wani makwabcin nasa kuma ya ce iyalan, mutanen kirki ne da ba su da abokin faɗa a ilahirin ƙauyen.
”Iyalai ne masu kirki da sanin ya kamata.”
Jasubhai Chaudhary ya ce shi da sauran ‘yan uwansa ba su san dalilin da ya sa ɗan uwan nasa ya tarkata iyalansa zuwa Amurka ba.
“Abin da muka sani kawai, shi ne sun tafi Canada, amma gaskiya babu maganar zuwa Amurka a lissafinsu kafin su bar nan,” in ji shi.
A watan Janairun 2022, an tsinci gawarwakin wasu iyalai huɗu ‘yan jihar Gujarat a sandare kusa da kan iyakar Amurka da Canada.
Jami’ai sun ce sun yi amanna cewa iyalan sun yi yunƙurin shiga Amurka ne.
Mutanen ƙauyen da ke arewacin jihar Gujarat sun shaida wa BBC cewa mutanen ƙauyen kan sanya burin zuwa ƙasashen waje a zukatansu, musamman Amurka, cike da fatan samun ingantacciyar rayuwa.
Wasu daga ciki ma kan faɗa hannun ɓata-gari, masu safarar mutane domin cimma burinsu.
‘Yan sandan Gujarat na ƙoƙarin kakkaɓe ayyukan masu safarar mutane a faɗin jihar.
Asalin hoton, PAVAN JAISHWAL
A watan Fabarairu ‘yan sandan sun kama mutum biyu kan zargin hannu a safarar wasu ‘yan ci-rani huɗu.
Masu kula da kan iyakar Amurka sun ce a ‘yan kwanakin nan ana samun matsaloli kan mutanen da ke ƙoƙarin tsallakawa ƙasar daga Canada.
Jami’an tsaron kan iyakar sun ce sun kama mutum 367, da ke ƙoƙarin tsallaka iyakar cikin watan Janairu kaɗai, fiye da adadin mutanen da suka tsallaka iyakar cikin shekara 12 da suka gabata.
‘Yan sandan Indiya sun shaida wa BBC cewa ba za su yi bincike kan mutuwar iyalan ba, har sai ‘yan sandan Canada sun nemi hakan daga gwamnatin Indiya.
“Suna da cikakkun takardun izini a lokacin da suka tafi Canada, don haka babu wani abu da za mu bincika”, in ji Dinesh Sinh Chauhan wani babban jami’i a rundunar ‘yan sandan ƙasar.