Dangote, gwamnoni da wasu yan majalisun tarayya sun ziyarci Buhari a Amurka


Yanzu haka tuni shugaban kasa Muhammad Buhari ya sauka a birnin Washington DC gabanin ganawar da zai yi da shugaban Amurka Donald Trump.

Cikin wadanda suka tarbi shugaban sun hada da gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, gwamnan jihar Ogun Ibikunle Amosun, ministan shari’a Abubakar Malami, Alhaji Aliko Dangote da kuma sauran mutane.

Ana sa ran tattaunawar da shugabannin biyu za su yi za ta mai da hankali kan sha’anin tsaro da kuma zuba jari.

Sai dai a wata hira da ya yi da yan jarida mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya zargi gwamnatin shugaban kasa Obama da ta gabata da gazawa wajen tallafawa Najeriya a yakin da take da ya yan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas na kasar.

Shehu ya ce gwamnatin ta bawa kasashen Nijer, Kamaru da kuma Chadi tallafi na miliyoyin daloli amma ta gaza bawa Najeriya saboda zargin da ta kewa sojanta na take hakin bil’adama.

You may also like