Dangote Ya Ce Harkar Noma Ne Kadai Zai Magance Rashin Aikin Yi A NajeriyaShugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya jaddada cewa rungumar harkar noma ne kadai zai magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasan kasar nan da suka kammala karatu a mataki daban daban.

Dangote ya ce a halin yanzu harkar kere-kere ta yi tsada ta yadda ba kowa ba ne zai iya shiga cikin harkar don haka ya nuna cewa hanya mafi sauki na magance talauce da kashe kashe wadanda akasari rashin aikin yi ke janyo shi ne a bunkasa harkar noma.

You may also like