Dangote Ya Nesanta Kansa Da Batun Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar PDPShugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya musanta Rahotanni da ake yayatawa kan cewa jam’iyyar PDP za ta tsayar da shi a matsayin dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019.

Dangote ya nuna cewa shi dai kasuwanci ne kadai ya sanya gaba ta yadda zai rika samar da ayyukan yi ga matasa inda ya nuna cewa masu hassada da irin ci gaban da ya samu ne ke yayata wannan jita jitar.

You may also like