Dangote Ya Samu Ribar Dala Biliyan Daya Cikin Kwanaki ShidaAlhaji Aliko Dangote mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Afirka, kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, ya samu karin dala biliyan daya da miliyan dari akan dukiyarsa cikin kwanaki shidan da suka gabata. 

Karuwar dukiyar ta Dangote na da nasaba da irin tagomashin da kasuwar hannun jari ta Najeriya take samu cikin yan kwanakin nan. 

Jaridar The Cable,ta gano cewa kasuwar ta samu ribar  naira tiriliyan daya da biliyan dubu dari shida, kuma kaso 30 cikin dari na wannan ribar zata koma hannun Dangote. 

Dangote da ya mallaki kaso 91 cikin hannun jarin kamfanin Simintin Dangote,kamfanin mafi girma da akafi hada-hadar hannun jarinsa a kasuwar,ya samu dagawar dukiyarsa daga dala biliyan goma(biliyan $10) a ranar 30 ga watan Mayun 2017,zuwa dala biliyan  goma sha daya ($11 biliyan), a lokacin da kasuwar ta rufe ciniki a ranar Litinin 5 ga watan Yunin 2017.

You may also like