DanGote Zai Gina Kamfanin Casar Shinkafa A Kano


Sannan kuma Zai Kaddamar Da Kamfanin Takin Zamani Mafi Girma A Afirka A 2017

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da cewa zai gina kamfanin casar shinkafa a Kano wanda zai rika amfani da shi wajen cashe shinkafar da ya noma a gonakinsa da ke jihohin Zamfara, Jigawa da Sokoto.

Haka ma, Attajirin ya bayar da sanarwar cewa zai kaddamar da kamfanin yin takin zamani a shekara mai zuwa wanda shi ne mafi girma a nahiyar Afrika kuma zai rika samar da tan 2.8 milyan na takin zamani a kowace shekara.

You may also like