DANKWAMBO YA GOYI BAYAN RUSHE RUNDUNAR SARS



Gwamnan Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya fito fili ya nuna goyon bayansa a ci gaba da kiraye kirayen da ake yi na rushe rundunar ‘yan sandan nan ta musamman na yaki ‘yan Fashi da makami wadda aka fi Sani da SARS.

Ya ce abin bakin ciki ne kan yadda rundunar ta koma aikin cin zarafin mutane a maimaikon kare lafiya da dukiyoyin jama’a inda ya kara da cewa akwai bukatar gudanar da garambawul ga rundunar ‘yan sanda baki dayanta.

You may also like