Danladi Sankara Ya Bada Tallafin Kudi Ga Mutanen Da Iftila’in Iska Ya Rutsa Da Gidajensu A Gumel


Tsohon Sanata Kuma Jigo A Jam’iyyar APC Ta Jihar Jigawa Dr Sanata
Danladi Sankara Ya Bada Tallafin Zunzurutun Kudin Har Naira Milyan Daya Ga Al’ummar Unguwar Dantanoma Dake Karamar Hukumar Gumel, Wadanda iftila’in Guguwar Iska Ta Fada Musu, Amatsayin Tallafinsa Na Gaggawa.

Tuni Kudi Ya Shiga Hannu Al’ummar Da Abun Ya shafa.

Haka Zalika Al’ummar Unguwar Sun Yabawa yan jaridu Bisa Watsa Labarin Abun Da ya Same su, Kuma Cikin Ikon Allah Suke Samun Taimako Daga Al’umma.

You may also like