Dara ta ci Gida


 

Bakaken kalaman da Dolnad Trump ya dinka amfani da su a matsayin makamai a wajen aibanta Musulmai da  sauran ‘yan adawansa sun janyo masa kazamar kyama daga gugun ‘yan jam’iyyarsa da dama.

An rawaito cewa yawan ‘yan jam’iyyarsa da ke ci gaba da yi wa masa kallon abin ki da kyama sai dada karuwa yake a kowace rana.

A sahun wadanda suka ce ba za kada wa shugabansu kuri’a ba akwai manya-manyan jiga-jigen jam’iyyar Republicain.

Mutanen dai sun kuduri juya wa masa baya ne tun bayan cin mutuncin wani Musulmi Ba’amurke da ya yi a ‘yan kwanakin da suka gabata.

Abinda da ya haifar da bacin ran Amurkawa, musamman ma ‘yan jam’iyyar Republicain wadanda suka dinka tambayar kawunansu ko ya dace su mara wa Trump baya.

A  yanzu dai da yawansu sun yanke shawarar kada wa shugabar Democrates Hillary Clinton kuri’a a yayin zabe mai zuwa.

You may also like