Darajar farashin Naira ta samu yunkurawa sama a Bankin canjin kudi na Najeriya. Kudin Naira na Najeriya ya samu dagawa da abin da ya kusa kai N1 a banki, sai dai kuma Naira ya sauka a kasuwar canji, Inji Hukumar Dillacin labarai na Kasa watau NAN
Darajar farashin Naira ta samu dagawa daga N304.5 zuwa N305 a kan kowace Dalar Amurka guda, ma’ana dai Naira ta kara daraja da Kobo 50 watau Rabin kwandala.
A kasuwar canji kuma, watau Bureau De Change, ana canjin dalar Amurka ne da Naira N385, yayin da kuma ake sayar da kudin Pound Sterling na Ingila a kan N560, ana kuma canjin Kudin EURO na Turai a kan N503 kan kowane guda.
Ma’ana dai Naira ta kuma fadi a kasuwar ‘Yan canji da ake kira Bureau De Change da har kusan N5 duk da cewa farashin Naira ya daga a Bankunan Kasar. Shugaban ’Yan Canjin na Kasa, Malam Aminu Gwadabe yace kwanan nan Darajar farashin Naira zai daga sama, domin kuwa Bankin Kasar na shirin yin wani abu a kan matsalar da ake fuskanta.