Darajar takardar kudin Naira tayi sama kadan, a kasuwar hada-hadar canjin kudaden kasashen waje ta bayan fage a ranar Laraba.
An siyar da takardar kudin na Najeriya N365 kan kowacce dalar Amurika guda $1 karin naira 1 kan yadda aka siyar da ita 365 a ranar Talata.
Kudin Pound na kasar Birtaniya ana sai da kowanne £1 kan N468 yayin da takardar kudin Euro tayi dai-dai da N412.
Masana tattalin arziki na alakanta tagomashin da takardar kudin ta Naira ke samu da yunkurin da babban Bankin kasa na CBN keyi na zuba kudade a kasuwar canjin kudaden domin ceto darajar Naira.