Darajojin Mata Guda 16 Da Suka Zarce Maza


(UUSIKUM FIN NISA’I KAIRA)
Inayi muku wasicci da Alkairi ga mata “Inji Manzon Allah {S.A.W} a cikin Hudubarsa ta ban kwana”

.
1) MACE ITACE tafara musulunta aduk duniya kuma tayiwa musulunci hidima da dukiyarta da duk abinda ta mallaka harda gwala gwalanta itace (NANA KHADIJA) (R.A).

.
2) MACE ITACE farkon wanda tafara Istimbabi a cikin shari’ar musulunci itace (NANA KHADIJA) R.a

.
3) MACE ITACE sanadiyyar samun taimama a shari’a (UMMUNA A’ISHA) R.a

.
4) MACE ITACE ta ilmantar da Sahabbai bayan wafatin Annabi {s.a.w} NANA A’ISHA (R.a).

.
5) MACE ITACE sanadiyar tsiran sahabbai daga fushin Allah lokacin da akai sulhun HUDAIBIYYA Kuma mace ce tashawo kan sahabbai har suka tsira daga fushin Allah.
(UMMU SALAMA) R.a

6) MACE ITACE ta kwantarwa Manzon Allah hankali lokacin da Ifk ya faru a madina, kafin saukar wahayi (BARIRA) R.a

.
7) MACE ITACE wanda Manzon Allah {s.a.w} yace idan mutum ya tarbiyyantar da ita koda bashine ya haife ta ba, zai shiga Aljanna shida Manzon Allah {s.a.w}.

.
8) MACE ITACE, tazamo ma’auni da mai Aure zai gwada kimarsa awajen Mahaliccinsa, idan ya kyautata mata yanada sakamako mai kyau, idan kuma ya cuceta akwai uquba daga Allah.

.
9) MACE ITACE shari’a ta tanadar mata ladan jam’in salloli guda biyar Da Juma’a da jana’iza da Jihadi, duk basai taje ba, amma sanadiyyar ta kyautatawa mijinta Allah zai bata duk ladan wadannan ibadun.

.
10) MACE ITACE sanadiyyar warware matsalar Zihari, suratul (MUJADALA).

.
11) MACE ITACE a duk qur’ani ba sura wacce aka saukar mai sunan maza sai mata suratun (NISA’I).

.
12) MACE ITACE tafara yin Sa’ayi tsakanin Safa da marwa (HAJARA).

.
13) MACE ITACE sanadiyyar tsiran mutanen sarauniyar Saba, suratul (NAML).

.
BILKISU MAI GADON ZINARE.
.
14) MACE ITACE sanadiyar musuluntar Sayyiduna Umar (R.a) (FATIMA).

.
15). MACE CE ake samun nutsuwa da ita !
LITASKUNU ILAIHA, Namiji bazai taba samun sukuni ba sai yanada mace !
.

16) MACE ITACE duk mulkin mutum da dukiyar sa sai da ita yake kara kima a idon mutane!

You may also like