Daraktan hukumar leken asiri ta Amurka (CIA), John Brennan, ya gargadi zababben shugaba kasar Donald Trump da ya nesanci maganganu marasa ma’ana da yake yi, don kuwa a cewarsa hakan lamari ne da zai taimaki harkokin tsaron Amurkan.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar Mr. Brennan, daraktan hukumar ta CIA, ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da tashar talabijin din Fox News ta Amurkan inda ya ce: Ina gani ya zama dole Mr Trump ya fahimci cewa wajibi ne yayi taka tsantsan cikin irin maganganu da yake yi dangane da matakan da kasar Rasha ta dauka a shekarun baya, yana mai maganganun nasa suna iya shafan tsaron kasar Amurkan.
Wannan dai ba shi ne karon farko da jami’an tsaron Amurkan suke sukan shugaban mai jiran gadon wanda yayi kaurin suna wajen maganganu musamman a shafinsa na Twitter da wasu suke ganin babu hikima da sanin ya kamata cikinsu.
Kalaman daraktan hukumar ta CIA na zuwa ne bayan fitar da wasu bayanan sirri da hukumomin tsaron Amurkan suka fitar kan cewa akwai yiwuwar shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi katsalandan cikin harkokin zaben shugaban kasa da aka gudanar a Amurkan lamarin da ya taimaka wajen lashe zabe na ba zata da Donald Trump din yayi.