Wani BAKANO ne dai ya je zance wajen yariyar da zai aura, bayan ta fito sun gaisa sai ga kananta da sabon kwano cike da damamar FURA mai sanyi damun bilanda.
BAKANONKA fa ya ji dadin kawo furar nan domin yana son shan fura sosai kuma dama da ‘yar yunwa sama-sama a jikinsa.
Budurwar ta bude kwano ta zuba ma BAKANO FURA a kofi. BAKANONKA ya fara shan fura yana hira. Ai kuwa bai ankara ba sai gardin fura ya ratsa shi, can BAKANONKA ya kalli budurwarsa ya ce “Kin san sunan ‘yar mu ta fari
kuwa Sweety?” Budurwar ta ce “a’a ban sani ba Darling!”
Da budar bakin gogan naka sai cewa ya yi ai “FURERA” za mu sa mata!