Daruruwan Gawarwakin Mayakan ISIS Sun Taru A Kasar Libiya Daruruwan gawarwakin mayakan ISIS, sun makale a kasar Libiya yayin da gwamnatin kasar ke tattaunawar mayar dasu kasashensu na asali.

Yawancin gawarwakin an kashe su a watan Disamba lokacin da sojojin kasar Libiya suka murkushe mayakan kungiyar ISIS a yakin da suka gwabza a garin Sirte  dake gabar ruwan bahar rum.

An dauke su zuwa birnin Misrata inda aka ajiye su a dakin a jiye gawarwaki dake birnin har zuwa yanzu.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, yawancin kasashen da mayakan suka fito suna jan kafa wajen karbar gawarwakin saboda hakan zai bayyana adadin yan kasarsu da suka bar gida domin shiga kungiyar yan ta’addar ta ISIS. 

Rahoton yace jami’an gwamnati a kasar Tunisia sunyi kiyasin cewa  yan mutane sama 3,000 ne da suka fito daga kasar suka shiga kungiyoyin yan ta’adda a kasashen Iraki, Syria da kuma Libiya.

Hukumomin kasar Libiya  sun dauki hotunan mutanen da kuma na gwajin kwayar halittarsu.

   Kungiyar mayakan ISIS ta karbe iko  da  birnin Sirte a shekarar 2015 ta kuma cigaba da rike birnin har zuwa watan Disambar shekarar 2016 lokacin dakarun sojin kasar ta Libiya suka karbe iko da birnin.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like