Dattawan Arewa Sun Fara Binciko Wanda Zai Maye Gurbin Buhari A 2019 



Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa kungiyoyi da dama a Arewacin kasar nan sun tura mutane zuwa wajen Atiku Abubakar, Ibrahim Dankwanbo (Gwamnan Gombe), Rabiu Kwankwaso, Sule Lamido, da Ibrahim Shekarau da nufin samun wanda zai tsaya takara ya maye gurbin Buhari.

Rahotanni na nuna cewa dalilin da ya haifar da hakan shi ne tsananin wahala da yunwa da ya addabi kasar musamman ma a yakin Arewa a yayin da Buhari ke mulkar kasar.

You may also like