Dattijuwa mai shekaru 113 ta fita kare martabar demokradiyya a Turkiyya

Wata dattijuwa Aisha Karabuber mai shekaru 113 a gundumar Turgutlu da ke lardin Manisa ta fita kare martabar demokradiyya don mayar da martani ga yunkurin juyin mulki da ‘yan ta’addar Fethullah Gulen FETO/PDY suka yi a ranar 15 ga watan Yuli.

‘Ya’yan dattijuwar ne suka kai ta dandalin da ake gudanar da zanga-zangar inda suka kai ta tsakiyar fili a kan keken marasa karfi.

Dattijuwar na dauke da tutar Turkiyya a hannunta da kuma hoton shugaba Recep Tayyip Erdoğan a wuyanta inda ta yi addu’a ga kasar Turkiyya.

Ta ce, ta san irin illar da juyin mulkin zai yiwa Turkiyya da a ce an yi nasara.

Karabuber ta kara da cewa, tana yi wa shugaba Erdoğan da dukkan mukarrabansa addu’a. Tana addu’ar Allah ts atsare kasarta da dukkan jama’arta ya kuma ba ta nisan kwana. Ta ce, ta dukkan juyin mulki da mulkin danniya da aka yi. Ta kuma san wanne hali jama’ar wancan lokacin suka shiga. Kar Allah ya sake nuna irin wannan lokaci. Kuma ta bukaci ‘ya’yanta su kawo ta wanna fili ne saboda ba ta son ta sake ganin wani juyin mulkin.

Ta zauna a dandal,in na wa daya inda daga baya ‘ya’yan nata suka sake daukarta zuwa gida.

You may also like