Sunansa Michael Adikwu wanda korarren dan sanda ne da aka taba kora a shekarar 2012 a garin Ilorin sakamakon saba doka.
Yana daga cikin ‘yan fashin da suka yi fashi tare da kashe rayukan jama’a da dama a yayin satan na garin Offa dake jihar Kwara. Rahotanni sun nuna cewa a jiya ya shiga hannun hukuma.