
Asalin hoton, Getty Images
Kwallon da Matthijs de Ligt ya ci ne ya sa Bayern Munich ta ci gaba da zama a matakin farko a teburin Bundesliga, bayan doke Freiburg.
Dan wasan tawagar Netherlands, mai tsaron baya, ya ci kwallon daga yadi na 25, bayan da ya Jamal Musiala ya bashi tamaula ranar Asabar.
Freiburg, wadda ta yi waje da Bayern a German Cup ranar Talata ta samu damar farke kwallo ta hannun Ritsu Doan, wanda ya buga kwallo ya bugi turke.
Haka kuma Yann Sommer ya hana kwallon da Roland Sallai ya buga ya fada raga.
Borussia Dortmund ta ci gaba da zama ta biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da kungiyar Thomas Tuchel, bayan da Dortmund ta ci Union Berlin 2-1.
Donyell Malen ne ya fara ci wa Dortmund kwallo, Kevin Behrens ya farke, sai matashin dan wasan Dortmund, mai shekara 18 Youssoufa Moukoko ya kara na biyu, wanda ya shiga canji.
Bayern ta lashe Bundesliga 10, wanda ta doke Dortmund 4-2 a makon jiya ta karbe matakin farko a babbar gasar tamaula ta Jamus.
Asalin hoton, EPA