
Asalin hoton, Getty Images
Declan Rice zai fi kowa tsada a tarihin cinikin ‘yan kwallo a Birtaniya idan zai bar West Ham United iin ji koci, David Moyes.
Chelsea ta dauki dan wasa daga Benfica, Enzo Fernandez kan fam miliyan 107 ranar Laraba.
Hakan ne ya sa dan kwallon tawagar Argentina ya zama wanda aka saya mafi tsada a Birtaniya a tarihi.
Rice dan wasan tawagar Ingila, mai shekara 24 ya yi wa West Ham karawa 224 tun bayan da ya fara taka mata leda a 2017, yanzu shi ne kyaftin a kungiyar.
”Ba makawa Declan zai zama fitatcen dan wasa,” in ji Moyes.
”Zai zama mafi tsada a kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon Birtaniya idan ya bar kungiyar.
Rice wanda ya koma West Ham ya fara daga karamar kungiyar a 2014, yanzu saura wata 18 yarjejeniyarsa ta kare a kungiyar.
Sai dai wasu rahotanni na cewar dan kwallon bai amince da sabon kunshin kwantiragin da aka gabatar masa ba, don tsawaita zamansa a kungiyar.
Fernandez, wanda ya lashe kofin duniya da Argentina a Qatar a 2022, mai shekara 22 ya koma Benfica daga River Plate.
Rice ya fara yi wa Ingila wasa tun 2018 a fafatawa da Jamhuriyar Ireland, shi kuwa Fernandez ya fara buga wa Argentina tamaula a watan Satumba.