Democrat ta tabbatar da takarar Hillary Clinton


 

Hillary Clinton ta kafa tarihi a kasar Amurka sakamakon amincewa da ita a matsayin yar takarar shugabancin kasar a babban taron Jam’iyyar Democrat.

Wannan shine karo na farko da aka zabi mace tayi takara a wanann matakin.

Hillary, tsohuwar matar shugaban kasar Amurka da kuma sakataren harkokin waje ta kai ga wannan nasara ne bayan doke abokin hamayarta Bernie Sanders a zaben fidda gwani.

Jiga-jigan jam’iyyar Democrat sun bukaci a fito kwai da kwar-kwata domin jefa wa Hillary Kuri’u a zaben shugaban kasa da zasu fafata da Trumph na Republican a watan Nuwamba.

You may also like