Wasu wakilai 6 daga Hukumar Kula da ‘yan gudun hijira ta kasar Denmark sun bayyana bukatar za su taimakawa Najeriya wajen kwakulo bama-baman da aka binne a yankin arewa maso-gabashin kasar.
A yayin wani taro da wakilan gwamnatin Tarayyar da na jihohi, wakilan na kasar Denmark sun ce, hakan zai taimaka wajen dawowar jama’a zuwa garuruwansu tare da komawa gonaki.
Shugaban Kula da ‘Yan Gudun Hijira na Denmark da ke Najeriya Shah Liton ya kai ziyara zuwa garin Bama inda Boko Haram ta kai hare-hare. A yayin ziyarar tasa ya gana da gwamnan jihar Borno Kashin Shettima inda suka tattauna kan batun sake gina yankin.
Shettima ya fara sanar da cewa, ya koma garin Bama da zama na wani dan lokaci, wanda a yanzu nan ne helkwatar runduna ta 21 ta sojin Najeriya.