
Asalin hoton, Getty Images
Luis Diaz zai koma buga wa Liverpool wasa a Elland Road a karawa da Leeds ranar 17 ga watan Afirilu, in ji Jurgen Klopp.
Diaz, mai shekara 26 ya fara jinya tun cikin Oktoban 2022, sakamakon raunin gwiwar kafa.
Dan kwallon tawagar Colombia ya koma atisaye, amma Liverpool ba za ta yi gangancin saka shi a wasa da Arsenal ranar Lahadi ba a Premier League.
”Yanzu yana cikin koshin lafiya, ya murmure, amma jinyar da ya yi mai tsawo ya sa sai mun yi taka tsan-tsan.” in ji Klopp.
”Yanzu mun tsara Luis zai fara buga mana wasan da za mu kara da Leeds, amma ba zai yi mana wanda za mu kara ranar Lahadi ba.”
Thiago Alcantara zai iya fafatawa da Arsenal, mai jan ragamar teburin Premier League a makon nan, wanda ya yi jinyar wata biyu.
Mai tsaron baya, Virgil van Dijk yana cikin ‘yan wasan da za su fuskanci Arsenal, bayan da bai buwa wasan da Liverpool ta tashi 0-0 da Chelsea a tsakiyar mako ba.
Arsenal tana matakin farko a teburin Premier da maki 72 da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester city ta biyu mai rike da kofin bara.
Liverpool tana matsayi na takwas da maki 43 a teburin Premier League, mai kwantan wasa daya.
Wasannin mako na 30 da za a buga a Premier:
Ranar Asabar 8 ga watan Afirilu
- Manchester United da Everton
- Aston Villa da Nottingham Forest
- Fulham da West Ham United
- Tottenham da Brighton & Hove Albion
- Leicester da Bournemouth
- Wolverhampton da Chelsea
- Brentford da Newcastle United
- Southampton da Manchester City
Ranar Lahadi 9 ga watan Afirilu
- Leeds United da Crystal Palace
- Liverpool da Arsenal