Diego Costa Ya Shirya Tsaf Dan Komawa Tsohuwar Kungiyar Sa Ta Atlentico Madrid Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake Kasar ingila, ya shirya tsaf dan barin kungiyar tun bayan sakon wayar da kocin kungiyar Antonio Conte ya tura masa na cewa baya bukatar sa a kungiyar a kakar wasanni da za’a shiga. 

Bisa wannan dalili ne yasa tsohuwar kungiyar tasa ta fara zawarcin dan wasan, shima kuma ya nuna karara cewar yana son komawa tsohuwar kungiyar tasa. 

Costa ya taimakawa chelsea taci kofin primiya ta bana inda ya zura kwallaye ashirin(20) a raga. A baya bayan nan ne kungiyar kwallon kafa ta Tainjin Dake Kasar chana taso siyen dan wasan amma yanuna baya son zuwa yafi son ya koma tsohuwar kungiyar sa ta Atlentico Madrid. 

You may also like