Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta Tsakiya, Sanata Dino Melaye ya sauya sheka daga jam’iyar APC zuwa PDP. Sanatan ya tabbatar da hakan ne zauren majalisar dattawa a yau inda ya canja kujerar zama daga bangaren masu rinjaye a majalisar wato APC zuwa bangaren PDP.
Dino Melaye dai a yau laraba ne ya dawo majalisar bayan shefa makonni ba ya majalisar tun bayan wani yunkuri da ya yi na tserewa daga hanun jami’an hukumar ‘yan sanda a lokacin da suke kan hanyarsu na kaishi Kotu inda ya dirko daga motar a yayin da take tafiya, wanda hakan ya kaishi ga gadon asibiti.