Direbobin motocin haya a Kaduna sun shiga yajin aiki


Direbobin motocin haya a Kaduna sun ki fitowa aiki yau saboda abinda suka ce cin muzguna musu da ma’aikatan KASTELEA suke yi a titunan garin Kaduna din.

Da gidan Jaridar Premium Times ta zagaya manyan titunan garin Kaduna din babu wani dan bus dake aiki.

Wani direba da ya zanta da wakilin mu a Kaduna ya ce ” muzgunawar ta yi yawa. Abinda yan KASTELEA ke yi mana ya isa haka. Baza mu iya hakuri da su ba.”

Mutane da ma’aikata suna ta sarar titi sanadiyyar rashin motocin kabukabu a garin yau.

Ma’aikatan KASTELEA kuwa duk sun watse a titunan garin Kaduna din.

Yanzu dai yan Keke Napep ne ke cin karensu ba bu babbaka. Sai yanda su ka yi da mutane.

Har yanzu dai gwamnati bata ce komai akai ba.

You may also like