Doguwa Na Dauke Da Bindiga Ne Lokacin Ziyararsa A Matsayin BakoABUJA, NIGERIA – Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriyar da a halin yanzu ke fuskantar shari’ar zarge-zargen kisan kai da tada rikicin zabe,

Kakakin hedkwatar rundunar tsaron Najeriyar, Brigediya Janal Tukur Gusau cikin wata sanarwa da ya aikewa Muryar Amurka, ya ce ana ta yada wannan hotone don a bata sunan sojojin Najeriya tare da zubda mutuncinsu a gaban ‘yan Najeriya ne.

Janar Gusau ya ce ainihin abin da ya faru shine an dau wannan hoto ne a dajin Falgore a wani sansanin horas da sojoji, yayin da BRIGADE na uku ke samun horo inda kuma aka gayyaci ‘dan majalisar a matsayin bako na musamman a lokacin.

Hedkwatar tsaron ta ce yana da kyau a sani yayinda duk aka gayyaci manyan mutane ire-iren wannan sha’ani akan girmamasu wajen basu bindiga su harba a matsayin bikin budewa amma ba da niyyar horas da su harbin bindiga ba.

Baiwa babban mutum bindiga ya harba wata daddadiyyar al’ada ce ta gidan soji yayin biki a ko’ina cikin duniya haka ake yi.

Alhassan Doguwa

Alhassan Doguwa

To amma hoton da aka bankado na Alhassan Ado Doguwa ake kuma kan yadawa a halin yanzu da zummar taba illar sojojin yayin da ake masu jinjina kan irin kyakkyawar rawa da suka taka yayin zaben shugaban kasa sai ga kuma wasu malaman addini suna sakin jawaban da ‘dan majalisar yayi inda suke baiwa jawabin wani mummunar fassara.

Sojojin suka ce hakan ka iya tada zaune tsaye da kuma ka iya kawo matsalar zaman dar-dar a daidai lokacin da ake kokarin mika mulki ga wata zababbiyar Gwamnati

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce ta tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa babu wani lokaci da ta taba baiwa wani farar hula horon harba bindiga ko makami don afkawa fararen hula.

Inda ta ce zata ci gaba da yin aiki tukuru kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar tana kuma neman jama’a da suyi watsi da duk wani kulle-kullen da ake son yi dangane da wancan faifan video na ‘dan majalisar.

Faifan videon dai na sake bulla a kafafen sada zumunta ne yayin da ake tuhumar ‘dan majalisar da zargin kisan kai da tada rikici yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a karamar hukumar Tudun wadan Jihar Kano, da ta kai ga har ‘yan sanda suka kamashi.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like