Dokar Hana Maza Marasa Hali Kara Aure Ba Ta Saba Musulunci Ba



Malaman addinin musulunci  sun fara tsokaci, game da bukatar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II ya aikewa majalisar dokokin jihar, kan yin dokar hana maza marasa hali kara aure.
Ustaz Hussein Zakariyya wani malamin addinin musulunci ne a Abujan Najeriya, ya bayyana  cewa dokar ba ta sabawa koyarwar addinin musulunci ba. Hasali ma wasu kasashen musulmai irin su Qatar, Jordan da kuma Bahrain sun yi irin wannan doka.
Ya yin da kasar Misra ta kafa wata karin dokar da za ta tilastawa namijin da ya bukaci sakin matarsa zuwa wurin limamin da ya daura auren ko wani na daban dan yin bayanin dalilan da suka sanya zai saki matar kafin hakan ta tabbata.
Ustaz Zakariyya ya kara da cewa wannan doka kusan mutanen jihar Kano kadai ta shafa, kama ta ya yi gwamnatin jihar ko Sarki Sunusi su yi dokar a matsayin dokar musulunci da ta shafi kowa.
Kafin kuma tabbatar da ita, ya kamata a fadakar da al’uma tare da wayar da kansu akan ainahin abinda ake bukatar su yi, sannan idan da hali a fara koyar da dalibai tun daga matakin sakandare har jami’a kan dokar.
A karshe ya ce kamata ya yi duk wani musulmi ya yi koyi da koyarwar addinin musulunci, da Kur’ani da Sunna, dan kaucewa sabawa Ubangiji. Tuni dai kwamitin da Mai martaba Sarkin Kano ya kafa ya ce yana yin aiki ne domin lalubowa jama’a hanyoyin sauki da tsara musu rayuwa bisa tanadin addinin musulunci.

You may also like