Hukumar Kwastan ta Kasa ta yi gargadin cewa duk wanda zai sayi sabuwar mota ya tabba cewa daga tashoshin jiragen ruwa a shigo da ita a yayin da dokar hana shigo da Motoci ta Iyakoki ta fara aiki.
A ranar 5 ga watan Disamba ne, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Janairu, an haramta shigo da Motoci ta iyakokin kasar nan ta jirgin ruwa. Rahotanni daga Iyakoki sun tabbatar da cewa akwai duban Motoci da suka makale a Kasahen da ke makwaftaka da Nijeriya.
Tuni dai kungiyar dillalan Motoci ta nemi gwamnati ta tsawaita wa’adin na watanni uku don ganin sun samu damar shigowa da duban Motocin da aka rigaya aka shigo da su ta kasashen da ke makwaftaka da Nijeriya.