Dokar Hana Shigo Da Motoci Ta Iyakoki Ta Gurgunta Tattalin Arzikin KwatanoMasu sayarda motoci a Cotonou babban birnin jamhuriyar Benin, sun koka da rashin cinikin motoci, tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da hana shigo da motoci na tokumbo daga iyakokinta na tudu.
Bincike ya nuna cewa sama da kaso casa’in da biyar na motocin tokumbo da ake sauke su a gabar tekun jamhuriyar Benin, masayansu na fitowa daga Nigeria ne mai makwabtaka da kasar.
Masu sayar da motocin sun ce yanzu kasuwar ta ja baya kuma farashin motocin ya sauko, saboda faduwar darajar Naira da kuma rufe iyakokin da Nigeriar ta yi wadanda suka taimaka wajen rashin samun cinikin motocin.
A baya dai jiragen ruwa na sauke kwantenoni ciki da motoci kamar dubu goma a wata,amma tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da sabuwar dokar,jirage a gabar tekun Cotonou suka ja baya inda a sati bai fi a sauke kwantenoni hamsin ba.

You may also like