Rahotanni sun nuna cewa sanarwar da gwamnatin Nijeriya ta bayar na hana shigo da Motoci ta iyakokinta, ya yi matukar tayar da hankalin kasashen da ke makwaftaka da Nijeriya inda suka turo wakilai don tattaunawa da jami’an gwamnatin. Nijeriya.
Haka nan kuma rundunar ‘yan sanda ta ki amincewa da izinin da kungiyar dillalan sayar da Motoci suka nema na gudanar da zanga zangar kin amincewa da wannan doka.
Kungiyar dillalan dai ta nuna cewa tana da ‘ya’ya sama da milyan biyu bayan ma’aikatan da ke ci karkashinsu sannan kuma a duk shekara suna samar da haraji ga gwamnati na kudi har Naira Bilyan 100.