A ranar 5 ga watan Disamba ne, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Janairun 2017, an haramta shigo da Motoci ta iyakokin kasar nan sai dai ta tashoshin jiragen ruwa.
Tuni wannan doka dai ta fara aiki. Hukumar Kwastan ta Kasa ta yi gargadin cewa duk wanda zai sayi sabuwar mota ya tabbatar cewa ta tashoshin jiragen ruwa aka shigo da ita.
Rahotanni daga Iyakoki sun tabbatar da cewa akwai duban Motoci da suka makale a Kasahen da ke makwaftaka da Nijeriya.
Kungiyar dillalan Motoci ta nemi gwamnatin tarayya da ta tsawaita wa’adin zuwa watanni uku don ganin sun samu damar shigowa da duban Motocin da ke kasashen da ke makwaftaka da Nijeriya inda ake jira kawai a shigo da su.