Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheik Aminu Daurawa ya yi ikirarin cewa sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa mata marasa aure sun kasu gida takwas.
Ya ce, kashi na farko su ne mafi yawan mata ‘yan siyasa ba su da aure, sai mafi yawan mata shugabannin makarantun sakandare, sai kashi na uku wadanda su ne, manyan sakatarorin gwamnati sai mata ma’aikatan gwamnati sai lauyoyi mata sai likitoci mata sai kuma mata ‘yan kasuwa sannan malaman jami’o’i mata sai na karshe ‘yan mata da ke makarantun sakandare da kwalejojin da kuma jami’o’i .
Ya kara da cewa idan har aka sanya wata doka wadda za ta takaita aure, wadannan mata za su kara shiga cikin wani mawuyacin yanayi.