Dole A Fara Yiwa Barayin Gwamnati Hukuncin Kisa – Farfesa Sagay


Shugaban Kwamitin Shugaban kasa Kan Bada Shawarwari Kan Yaki Da Rashawa, Farfesa Sagay Itse ya bayyana cewa lokaci ya yi da Shugaba Muhammad Buhari zai tanadi hukuncin kisa a kan barayin gwamnati.

Haka ma, Farfesa Sagay ya yi kira ga Buhari kan ya sallami wasu daga cikin ministocinsa wadanda ke yi wa shirye shiryen gwamnatinsa kafar-Angulu don ganin ya samu cimma nasarar aiwatar da ayyukan Jin dadin al’umma.

You may also like