Dole Buhari Ya Duba Korafin Mai Dakinsa – Majalisar Wakilai


‘Ya’yan majalisar wakilai na APC sun nuna goyon baya ga ikirarin Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari inda ta nemi mijinta ya sake duba salon mulkinsa tun kafin wasu tsiraru su karbe ikon jagorancin kasar nan.
A cewarsu, alkawurran da aka yi ‘yan kasa na sahihiyar canji yana neman ya zama mafarki kasancewa wasu sun yi katutu a gindin mulki tare da hana ruwa guda inda suka nemi a yi garanbawul a majalisar ministoci.
A bangarensa, Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana cewa an yi wa hirar da Aisha Buhari ta yi da BBC gurguwar fahinta inda ya ce manufarta shi ne na neman hadin kan ‘yan jam’iyyar da ke rikici da juna.
Haka ma, Gwamnan ya nuna cewa amsar da Buhari ya ba matarsa ba yana nufin ya kaskantar da jinsin mata ba ne yana mai cewa a gabansa Shugaban kasa ya yi wannan korafin na cewa aikin matarsa shi ne ta dafa masa abinci kuma ya yi shi ne a cikin raha

You may also like